BBC navigation

Najeriya za ta ci bashi daga China

An sabunta: 12 ga Satumba, 2012 - An wallafa a 20:30 GMT
Ngozi Okonjo Iweala, Ministar Kudi ta Najeriya

Ngozi Okonjo Iweala, Ministar Kudi ta Najeriya

Gwamnatin Najeriya ta ce za ta ciyo bashin kimanin dala billion daya da million dari daya daga kasar China .

Ministar kula da harkokin kudin kasar Ngozi Okonjo Iweala ta ce, Nigeria za ta yi amfani da kudin ne wajen gina filayen jiragen sama da layukan jiragen kasa masu sauri a babban birnin tarayyar kasar.

Haka kuma za a inganta harkokin sadarwar zamani a kasar.

Gwamnatin ta ce bashin yana da rangwamen kudin ruwa, kuma za ta biya shi ne cikin shekaru 20, tare da wani lamuni na karin shekaru 7 na biya.

Hukumomin na Najeriya suka ce za su kammala ayyukan da za su yi da kudin nan da shekara ta dubu biyu da sha biyar.

Sai dai wasu na ganin cewar da wuya a yi amfanin da kudin domin gudanar da ayyukan da aka ce za a yi da su.

Kari a kan wannan labari

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.