BBC navigation

Harin kunar bakin wake kan sabon shugaban Somalia

An sabunta: 12 ga Satumba, 2012 - An wallafa a 13:19 GMT
Sabon shugaban kasar Somalia, Hassan Sheikh Mohamud

Sabon shugaban kasar Somalia, Hassan Sheikh Mohamud

An kai harin kunar bakin wake a kofar Otel din da sabon shugaban kasar Somalia yake a Mogadishu, babban birnin kasar.

Wadanda lamarin ya faru a idonsu ne suka shaidawa BBC aukuwar al'amarin.

Dan kunar bakin waken da masu gadi hudu duka sun mutu a harin.

Rahotanni sun ce shugaba mai jiran gado, Hassan Sheikh Mohamud dake Otel din mai suna Jazeera a kusa da filin jiragen sama na kasar na cikin koshin lafiya.

Haka kuma akwai rahotannin karin fashewar wani abu a kusa da Otel din na Jazeera.

A ranar Talatar data gabata ne, kungiyar masu fafutukar Islama ta ce makiya Somalia ne suka shirya zaben da ya samu galaba.

Masu aiko da rahotanni sun bayyana zaben a matsayin wanda zai kawo karshen yakin da aka kwashe shekaru ana yi a kasar.

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.