BBC navigation

An kashe jakadan Amurka a Libya

An sabunta: 12 ga Satumba, 2012 - An wallafa a 11:17 GMT
Ambasadan Amurka a Libya, Christopher Stevens

Ambasadan Amurka a Libya, Christopher Stevens

Rahotanni sun ce ambasadan Amurka a kasar Libya ya mutu, bayan wani harin da masu dauke da makamai suka kai kan ofishin jakadancin Amurka dake birnin Benghazi.

Christopher Stevens na daga cikin jami'an ofishin hudu da aka kashe, a zanga-zangar nuna kin amincewa da wani fim na batanci ga Manzon Allah Sallallahu Alaihi wa sallam.

A wata sanarwa dake tabbatar da mutuwar ambasadan, wacce ta fito daga Amurka, shugaba Barack Obama ya yi tur da harin.

Wasu mutane ne mata da maza da ba a san ko su wanene ba, dauke da makamai suka far wa ofishin jakadancin Amurka da harbi da kuma bama-baman da aka kera na cikin gida.

Dakarun sojin Libya sun maida martani da harbe-harbe, amma kuma sun ce an ci karfinsu.

Dakarun sojin Libya sun ce ambasadan ya mutu a sanadiyar sikewar da ya yi.

Haka kuma an samu zanga-zanga a birnin Alkhahira na kasar Masar saboda fim din.

Babu hujjar kai harin

Tun da fari a wata sanarwa da aka fitar, sakatariyar harkokin wajen Amurka, Hillary Clinton ta tabbatar da mutuwar jami'i guda.

Tana mai cewa " Babban rashin ya sosa mana rai."

"Wasu sun bada hujjar aikata wannan mummunar dabi'a don daukar fansa game da wani abin da aka sanya a shafin intanet mai ta da hankali." Inji sanarwar.

Ta kuma kara da cewa "Amurka ba ta goyon bayan tozarta addinin wasu, amma zan fito karara in bayyana cewa babu wata hujja na tashin hankali."

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.