BBC navigation

Likitoci a Kenya na yajin aiki

An sabunta: 13 ga Satumba, 2012 - An wallafa a 15:42 GMT
Yajin aikin Likitoci

Likitocin Kenya na bukatar karin albashi

Likitoci a kasar Kenya sun fara yajin aiki, tare da zargin gwamnatin kasar da kin cika masu alkawarin da ta dauka na karin albashi da kyakkyawan yanayin aiki.

Yajin aikin ya shafi asibitoci da dama a cikin Kasar, inda ake kin karbar marasa lafiya da dama

Wadanda suke kwance a asibiti kuwa, na jira ne na tsawon sa'o'i kafin samun kulawa daga ma'aikatan kiwon lafiyar.

Likitocin sun ce an yi musu alkawarin karin kudaden alawus-alawus da karin albashi tun watan disambar bara, a lokacin da suka tafi wani yajin aiki.

Kari a kan wannan labari

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.