
IGP Muhammed Dahiru Abubakar shugaban rundunar 'yan sandan Najeriya
Rundunar 'yan sandan Najeriya ta umurci jami'anta da ke kasar baki daya da su kasance cikin shirin ko-ta-kwana sakamakon fushin da ai'ummar musulmi suka yi kan wani fim da aka fitar a Amurka.
Hukumar 'yan sandan kasar dai ta saka sansanoninta a duk fadin kasar cikin shirin dakile duk wata wutar rikicin da ka iya tashi; ganin yadda tarzoma ke barkewa a wasu kasashen musulmi, sakamakon fusata da al'umomin musulmin suka yi a wasu sassan duniya, bayan fitowar fim din da ya yi batanci ga Annabi Muhammadu (S.AW).
Wannan dai ya zo ne sa'oi bayan wasu musulmi sun gudanar da zanga zangar lumana a binin Jos na jihar Filato dake tsakiyar kasar a jihar dake fama da rikice-rikicen dake da nasaba da addini da kuma kabilanci.
Wata sanarwa da kakakin rundunar 'yan sandar Mr. Frank Mbah ya sanya wa hannu ta ce, Babban Sufetan 'yan sandan Mohammed Dahiru Abubakar ya umarci dukkan mukarrabansa dake shiyyoyi da kuma kwamishinonin 'yan sanda dake jahohi da su tabbatar da cewa an tsaurara tsaro a duk fadin kasar; musamman a ofisoshin jakadancin kasashen waje da sauran wuraren da rikici ka iya tashi.