BBC navigation

Ambaliya: wasu karin mutane 7 sun mutu a Najeriya

An sabunta: 13 ga Satumba, 2012 - An wallafa a 08:31 GMT

Wani wurin ambaliyar ruwa a Najeriya

Hukumomi a jihar Bauchi a Najeriya sun tabbatar da mutuwar mutane akalla bakwai a cikin wata ambaliyar ruwa da ta afkawa yankunan Zaki da Gamawa a farkon makon nan.

Wani jami'in watsa labaran gwamnatin jahar Abubakar Aliyu Wunti, ya fadawa BBC cewa baya ga asarar rayuka, dukiyoyi sun salwanta musamman ma gonaki.

Ambaliyar ta biyo bayan wani ruwan sama kamar-da-bakin-kwarya da aka yi a yankunan bayan fashewar wasu madatsan ruwa.

Wannan lamarin na faruwa ne yayin da kungiyoin agaji suka tabbatar da mutuwar wasu 'yan mata akalla goma a wani lamarin mai nasaba da ambaliya lokacin da kwale-kwalen da suke tafiya ciki ya kife a yankin Karin Lamido dake jihar Taraba.

Kari a kan wannan labari

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.