BBC navigation

Za a iya warware rikicin Boko Haram —Obasanjo

An sabunta: 13 ga Satumba, 2012 - An wallafa a 20:49 GMT
Olusegun Obasanjo

Tsohon shugaban kasar Najeriya, Cif Olusegun Obasanjo

Tsohon shugaban kasar Najeriya, Cif Olusegun Obasanjo, ya ce ya yi amanna za a iya warware rikicin Boko Haram ta hanyar lumana.

Cif Obasanjo ya bayyana hakan ne a wata hira da ya yi da Komla Dumor na Sashen Ingilishi na BBC.

Ga kadan daga cikin hirar, wacce tsohon shugaban kasar ya fara da bayani a kan yunkurin da ya yi na shiga tsakani don a kawo karshen matsalar ta Boko Haram a Najeriya:

Ni ne na dorawa kaina wannan aiki [na shiga tsakani] kasancewar na taba zama jagora a kasar kuma ina ganin har yanzu ina cikin wadanda za a kira jagororin kasa.

Wannan [rikicin] wani yanayi ne da ba mu saba da shi ba, saboda haka na tuntubi hukumomi cewa mai zai hana in je in gano abin da ke faruwa da ido na? Su kuma hukumomin ba su nuna rashin amincewarsu ba. Kuma abin da na gano na shaida musu.

To ’yan kungiyar ta Boko Haram sun mayar da martani ga wannan yunkuri naka ta hanyar kashe daya daga cikin mutanen da ka gana da su. Shin kana ganin akwai yiwuwar kawo karshen wannan al'amari cikin lalama?

Na yi amanna cewa komai rintsi, idan wadansu kungiyoyi biyu na mutane suna yakar juna to suna fatan samun hanyoyin warware matsalar cikin lumana.

"Na yi amanna cewa komai rintsi, idan wadansu kungiyoyi biyu na mutane suna yakar juna to suna fatan samun hanyoyin warware matsalar cikin lumana."

Obasanjo

Kuma ko ba komai, idan yakin ya kare dole ne a nemi hanyar fuskantar abin da zai biyo baya—kuma matsalar Boko Haram ba ta sha bamban sosai ba, in ka debe cewa kana fuskantar mutane ne wadanda ba su fayyace manufarsu ba.

To amma sun sha bayyana cewa manufarsu ita ce kafa shari’ar Musulunci a Najeriya. Ta yaya kake ganin za a sansanta da mutanen da ke so su dora tsarin wani addini a kan kasa irin Najeriya wadda al'ummominta ke da bambance-bambance da dama?

Shi ya sa na ce manufarsu ba a fayyace take ba: wadanda suka san tarihin Najeriya sun san cewa ba zai yiwu ka dora koyarwar wani addini ko ma akidar wani bangare a kan daukacin mutanen Najeriya ba.

Ya kamata wadannan mutane su san cewa wannan abu ne da ba zai yiwu ba—saboda haka wajibi ne a jawo hankalinsu su koma kan abin da zai yiwu.

Na yi amanna kamata ya yi a bullowa al'amarin ta fuska biyu—akwai inda ya kamata a hura akwai kuma inda ya kamata a ciza.

A matsayinka na tsohon shugaban kasa, ka amince cewa rashin kyakkyawan shugabanci ne—da gibin da ke tsakanin Arewa da Kudu ta fuskar ilimi da talauci—ya haddasa samuwar kungiyoyi irin su Boko Haram a Najeriya?

To, ba zan bayyana wannan abu cikin sauki haka ba—da wannan kam don wannan.

Kuma kamar yadda k ace akwai karancin ilimin zamani a Arewa—da ma kasar baki daya—da karancin ayyukan yi.

Dukkansu sun taimaka; amma kuma akwai wadansu dalilan daga waje: abin da ya biyo bayan rikicin Libya [misali].

Mutanen da suka samu horo a Libya lokacin [Kanar Muammar] Gaddafi, bayan faduwarsa sai suka warwatsu su da makamansu; irin abin da ke faruwa a arewacin Mali ke nan.

Kari a kan wannan labari

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.