BBC navigation

Kiristoci sun tir da fim din batanci ga Islama

An sabunta: 14 ga Satumba, 2012 - An wallafa a 08:23 GMT

Wasu kiristocin Najeriya suna addu'a a Cocin Nativity inda aka haifi Almasihu (A.S) wadda ke garin Beitlahem dake Falasdinu.

kungiyar kiristoci ta Najeriya CAN ta yi Allah -wa-dai da fitar fim din da aka yi a Amurka wanda ya ci zarafin addinin musulunci.

A wajen wani taron manema labarai a Kaduna, kungiyar ta CAN ta bayyana addinin Kiristanci a matsayin addinin da ke bukatar zaman lafiya da kwanciyar hankali wanda kuma yake gudun batanci ga mabiya wani addini.

Wannan dai ya zo ne yayinda ake ci gaba da zanga-zangar nuna rashin jin dadi ga wannan Film ko Majigi da ke nuna batanci ga Annabi Muhammadu S.A.W a wasu kasashe na musulmi.

Wannan wani bangare ne na kokarinda kungiyoyin addinai na musulmi da kiristoci a kasar ke yi na ganin batun wannan majigi bai haddasa wata sabuwar fitina tsakanin mabiya addinan biyu ba.

Kari a kan wannan labari

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.