BBC navigation

Manyan hafsoshin sojin kasashen ECOWAS na yin taro kan kasar Mali

An sabunta: 14 ga Satumba, 2012 - An wallafa a 15:36 GMT
'Yangwagwarmayar Islama na MUJAO a Mali

'Yangwagwarmayar Islama na MUJAO a Mali

Manyan hafsoshin sojojin kasashen kungiyar raya tattatalin arzikin Afrika ta yamma, wato ECOWAS ko CEDEAO sun fara wani taro na massanman a birnin Abidjan na kasar Cote-D'Ivoire don nemo hanyoyin warware rikicin kasar Mali.

Kungiyar ta ECOWAS ce dai ta shirya taron bayan kiran da Mali ta yi na a tura dakarun samar da zaman lafiya na MICEMA arewacin kasar inda 'yan tawaye suka mamaye.

Shi dai wannan taro na birnin Abidjan kan kasar Mali, zai kwashe kwanaki biyu ne ana gudanar da shi, game da maganar tura rundunar samar da zaman lafiya ta MICEMA a kasar

Taron zai dai tattauna ne kan kammala shirye-shiryen karshe na tura rundunar tsaro ta ECOWAS a kasar Mali, wato MICEMA , kamar yadda shugabanin kungiyar suka amince

Tuni dai kasar Mali ta nemi taimakon kungiyar ta Ecowas kan batun tura jami'an tsaron.

Haka nan kuma taron zai shirya aububuwan da kwamitin tsaro da sasantawa zai duba a ranar Litinin game da tura dakarun a kasar ta Mali.

Kari a kan wannan labari

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.