BBC navigation

Ana yi wa wasu tambayoyi kan kisan Jakadan Amurka

An sabunta: 14 ga Satumba, 2012 - An wallafa a 07:31 GMT

Ofishin Jakadancin Amurka a Bengazi bayan kai masa hari

Hukumomi a birnin Bengazi na kasar Libya sun ce suna tsare da wani adadi na mutane dangane da harin da aka kaiwa ofishin jekadancin Amurka da ke can ranar talata inda aka kashe jekadan Amurka.

Sabon Fara Ministan Libya Mustafa Abu Shakur ya shaida wa BBC cewar baya son kisan jekadan ya lalata dangatakarsu da Amurka kodayake yace mutanen kasar na da 'yancin bayyana fushinsu cikin lumana ga cin zarafinda aka yi wa addininsu a Amurka.

Amurkawa hudu da kuma 'yan kasar Libya goma ne dai aka kashe lokacinda masu zanga-zangar nuna rashin amincewa da fitar fim din batanci ga addinin Islama a Amurka suka afkawa ofishin a birnin Benghazi.

Wannan na zuwa ne a daidai lokacinda Shugaba Barack Obama na Amurka ya sha alwashin yin duk abinda ya wajaba wajen kare Amrkawa a kasashen waje, a daidai lokacinda zanga-zangar kan fitar Fim din batanci ga addinin musulunci ke kara bazuwa zuwa ofisoshin jekadancin kasar dake sauran kasashen Larabawa.

Kari a kan wannan labari

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.