BBC navigation

Mali: Red Cross na neman agaji daga mawadata

An sabunta: 14 ga Satumba, 2012 - An wallafa a 08:44 GMT

Wasu 'yan gudun hijira a Mali.

Kungiyar agaji ta duniya Red Cross ta yi kira ga mawadata da su taimaka mata da kudi kimanin Euro miliyan 20 domin ta ci gaba da ayyukan ta na agaji a yankin arewacin Mali.

Kungiyar tace tana bukatar kudin ne don tallafa wa dubban mutanenda ke cikin halin matsi da kayayyakin abinci da magunguna.

Rahotanni daga yankin na arewacin Mali dai na cewar dubban mutane na rayuwa cikin kunci sakamako hauhawar farashin abinci har yadda iyalai da dama ba zasu iya saye ba, yayinda kuma ma'aikatun gwamnati da ke samarda aiyukkan kiwo lafiya da masu samarda ruwan sha suka rurrufe saboda rashin ma'aikata.

Wannan shi ne Karo na biyu kenan da kungiyar agajin ta Red Cross ke yin kira don samun karin kudaden tafiyar da ayyukanta na tallafa wa al'umomin da yaki ya tarwatsa a arewacin Mali.

Kari a kan wannan labari

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.