BBC navigation

Hezbollah ta yi gangami a Beirut

An sabunta: 17 ga Satumba, 2012 - An wallafa a 09:03 GMT
Shugaban Hezbolla, Hassan Nasrallah

Shugaban kungiyar Hezbollah Hassan Nasrallah na yin kira a ci gaba da gudanar da zanga-zanga

Kungiyar nan ta 'yan Shi'a mai kaifin ra'ayin addinin Islama dake kasar Lebanon, wato Hezbullah ta yi wani gangami dazu a birnin Beirut inda ta nuna rashin amincewa da fim din nan da yayi batanci ga addinin musulunci.

Shugaban kungiyar Hezbullah, Sheik Hassan Nasrallah, wanda ya bayyana a wurin gangamin ya ce, dole ne gwamnatin Amurka ta dauki alhakin faifan bidiyon da ya fusata Musulmai tare da haddasa bacin rai a kasashen musulmai da dama.

Yana mai cewa ba ma a kan ofisoshin huddar jakadancin Amurka kadai yakamata a yi boren ba, har ma da yin matsin lamba ga gwamnatocin kasashen Musulmai domin su fito su nuna bacin ransu ga Amurka.

Sheik Nasrallah ya yi kira ga magoya bayansa cewa duniya na bukatar ganin bacin ransu, inda ya jaddada cewa lamarin zai shafi daukacin zaman lafiya a kasashen duniya.

Sheikh Nasrallah ya kuma bayyana faifan bidiyon a matsayin cin mutunci mafi girma da aka taba samu, kuma mafi muni fiye da littafin nan na ayoyin shaidan wanda marubucin nan Salman Rushdie ya rubuta, kuma aka buga a wata jaridar kasar Denmark a shakarar 2005 .

Kada a yi rikici

Sheik Nasrallah ya ce ''Yadda bacin ran ke cigaba da wakana dake sauya sabon salo, dole ne mu kara wayar da kan Musulmai da Kiristoci cewa kada su yi saurin fadawa cikin rikici a ko wace kasa.

"Wadanda za a dorawa alhaki na ladabtarwa da hukuntawa da kuma kauracewa, su ne wadanda suka shirya faifan bidiyon da kuma wadanda suke mara musu baya.'' Inji Sheik Nasrallah.

Yayin da dai zanga-zangar nuna kin jinin Amurka game da faifan bidiyon mai yin batanci da addinin Musulunci ke ci gaba da wakana a kasashe da dama, rahotanni sun ce daya daga cikin masu zanga-zangar ya rasa ransa a wata arangama da dakarun Pakistan dake wajen karamin ofishin huddar jakadancin Amurka a birnin Karachi.

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.