BBC navigation

Gwamnatin Najeriya za ta ba da lambobin yabo

An sabunta: 17 ga Satumba, 2012 - An wallafa a 09:23 GMT
Taswirar Najeriya

Taswirar Najeriya

A yau ne gwamnatin Najeriya za ta bada lambobin yabo ga wasu yan kasar sama da dari da arb'ain, sakamakon abin da ta ce gudummuwar da suke bayar wa ga cigaba kasa.

Gwamnatin dai ta ce za ta ba da lambobin girmamawar ne da nufin karrama wadanda aka zabo sakamakon irin gudummuwar da suke bayar wa wajen ci gaban kasar.

Bikin ba da lambobin girmamawa dai biki ne da aka saba da yin sa kusan ko wace shekara a Najeriya.

Manufarsa kamar yadda mahukunta kan ce ita ce karafafa gwiwar wasu 'yan kasar da suka ba da gudummuwa ga ci gaba Najeriya a fannoni daban-daban na rayuwa ba tare da la'akari da kowane irin bambanci ba.

Sai dai sannu a hankali wasu 'yan Najeriyar ciki har da wasu jam'iyyun adawa na ganin cewa martabar lambobin girmamawar na zubewa, bisa zargin cewa son zuciya a wajen zabar wadanda ake karramawar.

Wasu 'yan kasar na sukar cewa ba'a la'akari da cancanta a lamarin, kuma mafi yawan wadanda aka zabo magoya bayan jam'iyyar PDP mai mulkin kasar ne.

Sai dai mahukunta a kasar sun ce babu abin da ya hada masu zabo wadanda ake karramawar da jam'iyya mai mulki ko shugabannin kasar, don haka sukar da ake yi adawa ce kawai.

A 'yan shekarun dai mahukunta a Najeriyar na shan suka dangane da hanyoyin da kwamitocin da suke kafawa kan bi, wajen zabo wadanda ake karramawa da lambobin.

Wasu 'yan kasar dai na nesa-nesa da lambar girmamawar duk kuwa da cewa sun cancanta.

Irin wadannan mutane sun kunshi, shaharren mawallafin nan Chinua Achebe, wanda ya ki karbar lambar girmamawa ta commander of the Fefderal republic ko CFR har sau biyu, bisa zargin cewa mahukuntan kasar sun kasa magance matsalar cin hanci da rashawa da ta yi wa Najeriyar kanta.

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.