BBC navigation

Zaben 2015: Dattawan arewacin Najeriya sun kafa kwamiti

An sabunta: 16 ga Satumba, 2012 - An wallafa a 08:19 GMT

Dr. Muazu Babangida shugaban Dandalin Gwamnonin Arewacin Najeriya

Kungiyar Dattawan Arewacin Najeriya ta nada wasu kwamitoci da aka dorawa alhakin duba yanayin al'amurran siyasar kasar, tare da yin la'akari ta yadda za su yi daidai da bukatun yankin.

Batutuwan dai sun hada da sauye-sauye ga wasu bangarori na tsarin mulki da kuma rabon arzikin kasa.

kungiyar tace an dade ana amfani da wasu 'yan arewar ana kwarar jihohin arewar a al'amurranda suka shafi kasar.

Daya daga cikin wakilan kungiyar Farfesa Ango Abdullahi ya dora laifin kwarar da yace ana yiwa jahohin na arewa ga abinda ya kira sakacinda 'yan arewa dake majalisar dokokin kasar suka yi a baya.

Kari a kan wannan labari

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.