BBC navigation

Shugabanin Islama a Ghana sun tattauna da karamin jakadan Amurka

An sabunta: 17 ga Satumba, 2012 - An wallafa a 21:18 GMT
Musulmai na zanga-zangar nuna kyamar fim din.

Musulmai da dama a duniya sun nuna bacin ran su da fim din

A Accra babban birnin kasar Ghana yau an yi wata ganawa tsakanin karamin jakadan Amurka da ke kasar, Mr. Pat Alsup da shugabannin addinin musulunci a kasar karkashin jagorancin Babban Limamin kasar, Sheik Usman Nuhu Sharubutu.

Yayin taron dai bangaren shugabannin musulmin a Ghana sun bukaci gwamnatin Amurka ta janye fim din nan da ya yi batanci ga addinin musulunci, wanda aka shirya a Amurka.

A hirar da ya yi da manema labarai bayan ganawar, kakakin shugabannin Addinin Islama na Ghana, Alhaji Gado Muhammed ya ce Mr. Alsup ya shaida musu cewa shugaba Barack Obama tare da gwamnatinsa sun yi Allah wadarai da hoton bideon, kuma babu hannun gwamnatin Amurka wajen shirya fim din.

Ganawa tsakanin bangarorin biyu dai na zuwa ne bayan fim din da aka shirya a Amurka ya haddasa mummunar tarzoma a kasashe da dama, musamman na Larabawa.

Kari a kan wannan labari

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.