BBC navigation

Ana zaben cike gurbi a Kenya

An sabunta: 17 ga Satumba, 2012 - An wallafa a 21:02 GMT
Shugaba Kibaki

Shugaba Kibaki

Ana gudanar da wani zaben cike gurbi a Kenya, wanda aka bayyana da cewa wani zakaran gwajin dafi ne a siyasance ga wasu 'yan takarar shugabancin kasar a zaben da za'a yi badi.

Ana gudanar da zaben ne a yammaci da tsakiya da kuma yankin rift valley, wadanda wurare ne da suka fi sauran sassan kasar ta Kenya yawan kuri'u.

Pira minista Raila Odinga, wanda yana cikin wadanda za su yi takarar shugabancin kasar na fatan cewa, wannan zabe na cike gurbi zai taimaka wajen karfafa takararsa.

Sai dai kuma mataimakin Pira minista, Uhuru Kenyatta, wanda ke fuskantar tuhumar aikata muggan laifuka a gaban kotun hukunta manyan laifuka ta duniya, ICC shima yana fatan cewa, nasara a zaben cike gurbin zai zama wata alama ta amincewa da takararsa duk da tuhumar da yake fuskanta.

Kari a kan wannan labari

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.