BBC navigation

Kungiyar ECOWAS ta amince da daukar matakin soji a Mali

An sabunta: 18 ga Satumba, 2012 - An wallafa a 20:18 GMT
Taron Ministocin Harkokin waje na ECOWAS

Taron Ministocin Harkokin waje na ECOWAS

An kammala wani taron Ministocin harkokin waje daga kungiyar kasashen Yammacin Afrika - ECOWAS, a Abidjan babban birnin Ivory Coast.

Sun amince da wani shirin daukar matakin soji a kan rikicin kasar Mali.A yanzu an shafe watanni tun lokacin da masu fafutukar islama suka kwace iko da arewacin kasar Mali.

Bayan kwashe tsahon lokaci, Kungiyar ECOWAS ta amince ta aike da dakarunta dubu uku domin su yaki masu fafutukar. Dakarun za su fito ne daga kasashen Ivory coast, Senegal, Togo da kuma Niger.

A Kwanakin farko-farko na ganawar manyan hafsoshin sojin kasar ne suka tattauna game da tsare-tsaren, yayin da ministocin tsaro da na harkokin kasashen waje suka amince tsarin.

Dalilin da ya sa aka samu jinkiri sosai shi ne, tun da fari gwamnatin Mali ba ta fito ta bayyana cewa ba za ta iya magance matsalar da kan ta ba. A yanzu haka masu sharhi sun ce shugaban Mali Diyokonda Tirori ya na son a tura dakarun kasashen ketare ne, amma prime ministan kasar Cheik Modibo Diarra baya goyon baya.

Haka nan akwai takaddama kan cewa ko za a kafa sansanin dakarun ne a Bamako ko kuma za su wuce kai tsaye arewacin kasar ne.

Kasar Mali na cikin tashin hankali tun lokacin da aka yi juyin mulki a a ranar 22 ga watan maris din wannan shekara, a lokacin da aka hanbarar da gwamnatin tsohon shugaban kasar Ahmadou Toure Tounami.

Duk da cewar sojojin da suka jagoranci juyin mulkin sun mika mulki ga gwamnatin farar hula, amma har yanzu ana ganin su na da matukar tasiri wajen gudanar da al'amuran kasar da kuma rundunar sojan kasar wadda ta nuna kin amincewa da matakin sojan. Wata kungiya ta 'yan siyasa da ake kira MP22 wadanda suke goyan bayan juyin mulkin, sun yi zanga-zangar kin amincewa da matakin sojan, tare da cewar ba sa bukatar dakarun kasashen waje a Mali.

Kari a kan wannan labari

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.