BBC navigation

Mutane 12 har da 'yan Afrika ta Kudu sun mutu a harin Kabul

An sabunta: 18 ga Satumba, 2012 - An wallafa a 10:55 GMT
Harin kunar bakin wake a birnin Kabul

Harin kunar bakin waken da aka kai a birnin Kabul

Harin kunar bakin wake a kan wata mota a Kabul dake Afganistan ya hallaka mutane goma sha biyu ciki har da 'yan Afrika ta Kudu takwas.

Wata 'yar kunar bakin wake ce ta tarwatsa karamar motar safa a bakin hanyar da ke kusa da filin saukar jiragen sama na Kabul, babban birnin kasar Afganistan.

Kungiyar nan mai fafutukar Islama ta Hezb-e-Islami ce ta dauki alhakin kai harin, wanda ta ce na nuna bacin rai ne game da faifai bidiyon nan na batanci ga addinin Musulunci.

Jami'an 'yansanda dake birnin Kabul sun ce 'yar kunar bakin waken dake cikin wata mota ta daban, ta tunkuri motar safar dake da fasinjojin da suka ce da alamu yana biye da ita ne kafin ta afka mata.

Baya ga fasinjoji goma sha ukun da suka hallaka , harin kuma ya yi sanadiyyar mutuwar wani mai wucewa a bakin hanyar da kuma wani makanike.

Yayin da kuma wasu masu gadin hukumar tsaron farin kaya ta kasar biyu suka jikkata.

Wani ganau a yankin ya shaida wa BBC cewa fashewar na da karfin gaske, ya kuma ce karamar motar safar dake dauke da ma'aikatan ta tsaya a wani gidan mai dake kusa da gidansa ne kafin daga bisani maharin da yake biye da su a wata mota ya abka musu.

Jami'an tsaron dake birnin Kabul sun ce suna bincike game da mummunan harin.

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.