BBC navigation

Kotu a Faransa ta haramta kara buga hoton matar Yarima William ba riga

An sabunta: 18 ga Satumba, 2012 - An wallafa a 15:59 GMT
Uwargida Kate Middleton

Uwargida Kate Middleton

Wata kotu a Faransa ta yanke wani hukunci dake haramta ci gaba da bugawa, ko raba hotunan matar Yerima William, na biyu a jiran gadon sarautar Birtaniya, tana kwance a rana, kirjinta a bude.

Wata kotun majistare dake kusa da birnin Paris ta bada umurni ga gidan mujallar Closer ta Faransa, inda aka fara buga hotunan da ya mika dodon hotunan cikin sa'o'i ashirin da hudu.

Sun ce duk wanda ya karya ka'idar zai biya tarar euro dubu goma.

Masu gabatar da kara na Faransa ba su tabbatar da ko wannan mataki zai bada wata kafa ta gurfanar da mujallar da ta fara buga hotunan, ko ma shi mai daukar hoton da ya dauki Yarima William da mai dakin tasa, lokacin suna hutu a Faransa, a gaban kotu ba.

Yariman da mai dakinsa sun yi marhabin da hukuncin.

Kari a kan wannan labari

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.