BBC navigation

Rundunar da NATO ke jagoranta zata rage ayyukan hadin gwiwa da sojin Afghanistan

An sabunta: 18 ga Satumba, 2012 - An wallafa a 15:40 GMT
Sojojin NATO a Afghanistan

Ana kashe dakarun NATO sama da 50

Rundunar da NATO ke jagoranta a Afghanistan ta ce zata yi matukar rage yawan ayyukan hadin gwiwa da su ke yi da rundunar sojan Afghanistan, a matsayin martani kan karuwar da aka samu na irin hare haren da dakarun Afghanistan ke kaiwa a kan abokan aikin nasu na kasashen waje

Mai magana da yawun rundunar tsaron ta NATO, Birgediya Janar Gunter Katz ya bayyana cewa babban kwamandansu ya ce , a nan gaba, dakarun kawance zasu yi aiki da na Afghanistan ne kawai a wasu lokuta na muhimman ayyukan samame, kuma duk wani karamin aikin sintiri ko samame na hadin gwiwa a gaba, sai ya samu amincewar wani babban kwamanda.

A bana dai dakarun Afghanistan sun kashe dakarun NATO sama da hamsin.

Kari a kan wannan labari

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.