BBC navigation

Majalisar wakilan Najeriya ta soki yunkurin kirkiro da takaddar kudi ta 5,000

An sabunta: 18 ga Satumba, 2012 - An wallafa a 16:18 GMT
Mallam Sanusi Lamido Sanusi

Babban bankin Najeriya na yunkurin kirkiro da sabuwar takaddar kudi

A Najeriya, a yau ne Majalisar wakilan Kasar ta koma aiki bayan wani dogon hutu da wakilanta su ka yi.

Daya daga cikin abubuwan da 'yan majalisar su ka tafka mahawara akai dai shine yunkurin nan da babban bankin Najeriyar yake yi na kirkiro da sabuwar takaddar kudi ta 5,000 inda kuma ta bayyana rashin gamsuwar ta

Majalisar wakilan dai ta bayyana cewar batun kirkiro da sabuwar takardar kudin yazo mata ne ba shiri, kuma ta ce ba a sanya ta cikin maganar ba

Majalisar wakilan ta kara da cewar batun ya janyo korafe korafe daga bakunan 'yan Najeriya, a don haka tace wani batu ne da 'yan Najeriya basa maraba da shi

'Yan majalisar sun kuma bayyana cewa tsarin kirkiro da sabuwar takaddar kudin, zai kara sanya 'yan Najeriya ne cikin talauci, kuma tace mataki ne da zai janyo harhawar farashin kaya

A don haka majalisar tace zata gayyaci gwamnan babban bankin Najeriyar ko wasu jami'ai domin suzo suyi wa majalisar bayani

Kari a kan wannan labari

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.