BBC navigation

Yan sanda a Afrika ta Kudu sun tarwatsa masu bore

An sabunta: 19 ga Satumba, 2012 - An wallafa a 13:45 GMT
Motar 'yan sanda a Marikana

Motar 'yan sanda a Marikana

'Yan sanda a kasar Afrika ta Kudu sun yi amfani da albarusai na roba da hayaki mai sa hawaye wajen tarwatsa masu hakar ma'adanai dake zanga-zanga.

Al'amarin ya faru ne a kusa da mahakar ma'adanai ta Marikana, kwana daya bayan an cimma yarjejeniyar da ta kawo karshen yajin aikin masu hakar ma'adanan.

Kakakin 'yan sandan ya ce " Ba za mu amince da duk wani gangami da ba a bisa ka'ida yake ba. "

Masu hakar ma'adanai na Marikan sun janye daga yajin aikin bayan sun amince da karin albashi na kashi 22 cikin dari.

Yajin aikin dai ya bazu zuwa wasu mahakan ma'adai dake Afrika ta Kudu, kasar dake cikin kasashen da suka fi samar da ma'adanai masu daraja.

A ranar Litinin ne, shugaba Jacob Zuma ya ce yajin aikin na Marikana ya janyo asarar dala miliyan 548 ga fannin hakar ma'adanai.

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.