BBC navigation

An soma jigilar Alhazai daga Najeriya zuwa Saudiyya

An sabunta: 19 ga Satumba, 2012 - An wallafa a 20:10 GMT
jirgin

Maniyyata aikin hajji sun soma tafiya Saudiya daga Najeriya

An soma jigilar maniyyatan Najeriya zuwa kasar Saudiyya domin gudanar da aikin hajjin bana.

An dai gudanar da wani kwarya -kwaryan biki a filin jirgin sama na Malam Aminu da ke Kano kafin tashin jirgin farko da ya kama hanya zuwa kasar ta Saudiyya.

A duk shekara dai an saba fuskantar matsaloli dangane da jigilar alhazan da kuma zaman su a kasa mai tsarki.

Jakadan Najeriya a kasar Saudiya, Ambasada Abubakar Shehu Bunu ya ce sun kamalla shirye shiryen ganin cewar 'yan Najeriya sun gudanarda ibadunsu cikin sauki a kasa mai tsarki.

Kari a kan wannan labari

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.