BBC navigation

Obama ya zargi Romney da aibata Amurkawa

An sabunta: 19 ga Satumba, 2012 - An wallafa a 07:34 GMT
Barack Obama da Mitt Romney

Shugaban Amurka Barack Obama da abokin karawarsa Mitt Romney

Shugaba Obama ya zargi abokin karawarsa Mitt Romney, da aibata wani babban bangare na Amurkawa, bayan ya furta kalaman kaskanci ga wasu masu kada kuri'a.

Mista Romney ya furta kalaman kaskanci ne a wani taron liyafar cin abincin dare na tara kudi.

A wani shirin tattaunawa na gidan talabijin, Mr Obama ya ce daya daga cikin abubuwan da ya koya a matsayinsa na shugaban kasa shine ya kamata ya wakilici daukacin jama'arsa.

Bayan da aka zabe shi, ya ce yayi azama wajen yin alkawarin cewa zai yi aiki tukuru ga jama'a har ma wadanda ba su zabe shi ba.

Yace '' Abu daya da na koya shine, ka wakilici daukacin jama'ar kasarka.Kuma lokacin da na hadu da yan jam'iyar Republican yayin da nake zagayawa cikin kasar, na lura cewa suna da kwazo, kana iyalai ne da suke kishi da kaunar kasarsu.Ni a tunani na idan kana son zama shugaban kasa to kamata ya yi ka yiwa kowa da kowa aiki, ba wai wasu 'yan tsiraru ba.''

An dai bayyana cewa, kalaman na Mr Romey, wanda da aka yada a shafin yanar gizo ya nuna karara cewa ana nufin yin nakasu ga mai kalubalantar na jam'iyar Republican, yayinda ya rage saura kasa da watanni biyu a fara gudanar da zaben shugaban kasa.

Kari a kan wannan labari

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.