BBC navigation

Fada ya kara rincabewa a Syria

An sabunta: 19 ga Satumba, 2012 - An wallafa a 15:43 GMT
Fada a Syria

Fada a Syria

Mummunan fada ya kara rincabewa a Damascus, babban birnin Syria, inda rahotanin ke cewa dakarun gwamnati na kara dannawa kusa da anguwar Al Hajar Al Aswad.

Wakilin BBC ya ce, gidan talabijin na hukuma ya nuna yadda dakaru suka yi ma anguwar ta Al Hajar al Aswad dake kudancin Damascus, tsinke.

Masu fafutuka sun ce an kashe mutane sama da ashirin nan take, a anguwar.

Haka nan kuma wani sabon fadan ya barke a Aleppo , birni mafi girma a kasar.

Can kuma a kan iyakar kasar da Turkiyya, 'yan tawaye sun karbe iko da kan iyaka, sun kuma sauke tutar kasar Syriar.

A birnin Damascus, Ministan harkokin wajen Iran, ya tattauna da shugaba Assad da ministan harkokin wajensa kan tashin hankalin.

Kari a kan wannan labari

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.