BBC navigation

Karancin abinci na kashe miliyoyin kananan yara - UNICEF

An sabunta: 19 ga Satumba, 2012 - An wallafa a 08:41 GMT
Yara na karbar abinci a kasar Somalia

Yara a kasar Somalia na karbar taimakon abinci daga UNICEF

Yayin da miliyoyin kananan yara ke ci gaba da fama da cututtuka da kuma karancin abinci a kasashe da dama na nahiyar Afirka ciki har da Nijeriya, Asusun kula da yara na majalisar Dinkin Duniya wato UNCEF, ya shirya wani taro na manyan masu tsara manufofi daga gwamnatoci a kasar.

Taron dai an yi shi ne a garin Lafiya babban birnin Jihar Nasarawa da nufin duba batun karancin abinci a kasashen yankin Sahel.

Shiyya ta hudu ta UNICEF ce ta shirya taron ga jihohi goma na arewacin kasar wato jihohin Borno da Yobe da Kano da jigawa da Bauchi da Gombe da Taraba da Adamawa da Filato da kuma mai masaukin baki wato jihar Nasarawa.

An kuma tattauna a kan matsalar karancin abinci mai gina jiki da kananan yara ke fama da shi musamman a Afirka, da kuma yadda za a samu hadin gwiwa da gwamnatoci goma da abin ya shafa.

Talauci na daya daga cikin abin da masana suka bayyana cewa na haifar da matsalar karancin abinci mai gina jiki a tsakanin yaran da ma iyayensu a Afirka.

Asusun kula da yaran na Majalisar Dinkin Duniya UNICEF ya ce akwai bukatar samar da abin yi ga iyaye mata ta yadda za su rika samun kudaden shiga da zai taimaka wajen watadar abincin mai gina jiki.

Kari a kan wannan labari

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.