BBC navigation

An baiwa Aung San Suu Kyi lambar yabo a Amurka

An sabunta: 20 ga Satumba, 2012 - An wallafa a 08:31 GMT
Aung San Suu Kyi

Jagorar yan adawar kasar Aung San Suu Kyi

Jagorar adawa a kasar Burma Aung San Suu Kyi, ta karbi lambar yabo ta zinari mafi girma a kasar Amurka, lambar da aka riga aka bata tun tana daurin talala a shekara ta 2008.

Jim kadan bayan karrama Miss Suu Kyi din ne kuma, shugaban Amurka Barack Obama ya sanar da dage takunkumin da aka kakaba wa shugaban kasar Burma, Thein Sein.

Inda Obama ya tabbatar wa da Aung San Suu Kyi cewa Amurka za ta cigaba da taimakawa kasar Burma wajen kawo sauye-sauye.

Lokacin da ake gudanar da bikin bayar da lambar yabon, sakatariyar harkokin wajen Amurka, Hillary Clinton ta yabawa Aung San Suu Kyi cewa mace ce mai kwazo wajen rajin kare hakkin bil'adama da dimokaradiyya.

Miss Suu Kyi ta bayyana matukar godiyarta, inda ta ce wannan wata rana ce da ba za ta taba mantawa da ita a rayuwarta ba.

Bayan dage takunkumi dai, ana sa ran zuwan shugaba Thein Sein na Burmar zuwa Amurka a mako mai zuwa domin halartar babban taron Majalisar Dinkin Duniya.

Kari a kan wannan labari

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.