BBC navigation

N5000: Babban Bankin Najeriya ya dakatar da shirinsa

An sabunta: 21 ga Satumba, 2012 - An wallafa a 06:08 GMT
Babban Bankin ya sha suka daga wajen 'yan kasar

Kudin Najeriya

A Najeriya, Babban Bankin kasar ya dakatar da shirinsa na fitar da sabuwar takardar kudi ta N5000 da kuma mayar da wasu takardun kudin sulalla da ya so ya yi a shekara mai zuwa.

Babban Bankin Najeriyar, ya ce ya dauki wannan mataki ne bayan da ya samu umarni daga shugaban kasar Dr Goodluck Jonathan.

Babban Bankin ya musanta zargin da wasu ke yi cewa tuni ya bayar da kwangilar buga takardun kudin.

Batun ya jawo zazzafar muhawara a kasar inda ko da Majalisun Dokoki sai da suka umarci Babban Bankin ya dakatar da shirin, suna masu cewa zai kawo hauhawar farashin kayayyaki.

Babban Bankin ya sha suka

A wata sanarwa da Babban Bankin ya fitar ya ce dokar da ta kafa shi ta ba shi damar kirkirar kudin takarda, ko sulalla, bisa yarjewar hukumar gudanarwarsa da kuma amincewar shugaban kasa.

Sanarwar, wacce Daraktan Sadarwa na Babban Bankin, Ugo Okoroafor, ya sanyawa hannu ta kara da cewa hakan ne ya sanya Babban Bankin ya nemi amincewar shugaba Goodluck Jonathan a watan Disamabar shekarar 2011, domin ya fitar da takardar kudin ta N5000 da kuma mayar da wasu takardun kudin sulalla, da zummar inganta tsarin kashe kudi a kasar.

Sai dai Babban Bankin ya ce ya samu umarni daga shugaba Goodluck Jonathan a ranar Alhamis kan ya dakatar da shirin nasa.

A watan jiya ne Babban Bankin Najeriyar ya bayar da sanarwar cewa zai fito da sabuwar takardar kudi ta naira dubu biyar a cikin jerin kudaden kasar da ake hada hadar kasuwanci da su.

A cewarsa, sabuwar takardar kudin za ta kasance dauke ne da hoton fuskokin wasu fitattun mata uku a Najeriya; wato Margaret Ekpo, da Hajia Gambo Sawaba, da kuma Funmilayo Kuti.

Sai dai Babban Bankin ya sha suka daga wajen 'yan kasar bisa wannan aniya tasa, inda akasarin mutane ke cewa matakin zai kawo hauhawar farashin kayayyaki da kara jefa su cikin matsin tattalin arziki.

Su ma Majalisun Dokokin kasar sun yi tur da matakin, inda a makon da muke ciki, suka bai wa shugaban kasar umarni na ya dakatar da babban bankin daga aiwatar da shirin nasa.

Kari a kan wannan labari

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.