BBC navigation

Ma'aikatan hakar ma'adanai a Afrika ta Kudi sun koma bakin aiki

An sabunta: 20 ga Satumba, 2012 - An wallafa a 07:56 GMT
Ma'aikatan Mahakar Ma'aidinai na kasar Afirka ta Kudu

Ma'aikatan Mahakar Ma'adinai ta kasar Afirka ta Kudu

Mahakan ma'adanai a Afrika ta Kudu sun koma wurin aikin hako ma'adanan Platinum, inda akayi mummunar zanga-zangar da mutane 40 suka mutu, lokacin yajin aikin tsawon makonni shidda, wanda hukuma ba ta amince da shi ba.

Mahakan, wadanda ke ta fito da bushe-bushe lokacin da suke komawa aiki.

Sunce suna murna a kan karin kashi 22 bisa dari na albashi da aka yi masu, duk da cewa bai kai yawan abinda suka nema ba.

Daya daga cikin ma'aikatan ya bayyana farin cikinsa:

Ya ce; "Ina murna sosai cewa zan koma aiki yanzu. Zan kuma yi rawuta cikin jin dadi yanzu".

Wasu mahaka zinari, su dubu 15 ma, suna yajin aikin neman irin wannan karin albashi.

Kari a kan wannan labari

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.