BBC navigation

Zanga-zangar fim ta yi muni a Pakistan

An sabunta: 21 ga Satumba, 2012 - An wallafa a 15:41 GMT
Zanga zanga a Pakistan

Zanga zanga a Pakistan

A Pakistan an yi arangama tsakanin 'yan sanda da mutanen dake zanga zangar nuna bacin rai game hoton Videon nan da aka hada a Amurka mai nunin kin jinin musulunci.

Akalla mutane goma sha biyar ne suka mutu ciki harda yayin da wasu da dama suka samu raunuka.

Daga cikin wadanda suka rasa rayukansu harda wani ma'aikacin gidan Talabijin na Pakistan a Peshawar a lokacin da yansanda suka bude wuta domin tarwatsa masu zanga-zangar da ke kokarin kona wani gidan Sinima.

Taron mutane cike da fushi a Karachi sun kai hari a kan bankuna da gidajen Silima, kuma rahotanni sunce dansanda akalla daya ne aka kashe.

Dubban masu zanga zanga sun yi kokarin su kai kusa da da'irar gine -ginen ofisoshin Diplomasiya mai matsanancin tsaro a Islamabad babban birnin kasar a inda Ofishin Jakadancin Amurka yake.

Gwamnati dai ta ayyana yau Juma'a a matsayin ranar hutu , ta kuma bukaci mutane da su yi zanga zanga cikin ruwan sanyi.

Tun farko dai Ma'aikatar harkokin wajen Amurka ta kashe dala 70000 a kan tallace-tallacen da ta bayar a gidajen talabijin na kasar Pakistan da zummar rage kaifin bacin ran da wani fim da aka yi a kasar, wadanda ya yi batanci ga addinin musulunci, ya jawo.

Tallace-tallacen sun nuna shugaba Obama da Sakatariyar wajen Amurka, Hillary Clinton na yin Alla-wadai da fim din.

Mista Obama ya bayyana Amurka da cewa kasa ce da ke mutunta kowane addini don haka ba ta da muradin cin zarafin kowane addini.

Ita ma Sakatariya Clinton ta ce gwamnatin Amurka ba ta da hannu a shirya fim din wanda aka yi a jihar Califonia.

Kari a kan wannan labari

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.