BBC navigation

An kashe masu gadi 4 a wani gawurtaccen harin bam a Damascus

An sabunta: 26 ga Satumba, 2012 - An wallafa a 16:35 GMT
Harin bam a Syria

Harin bam a Syria

Jami'an Syria sunce an kashe masu gadi 4 tare da raunata wasu mutanen 14 a wani gawurtaccen harin bam da ya lalata Hedikwatar soji matuka a tsakiyar Damascus.

Jami'an tsaro sun shedawa Gidan Talabijin na kasa cewar wasu yan kunar bakin wake da bama bamai a mota ne suka tayar da bama baman, wanda ya sa ginin ya kama da wuta.

Daga nan kuma harbe harben bindiga sun kaure a ciki da zagayen ginin , yayinda yan tawaye suka afka masa.

Jami'an gwamnatin Syrian sun ce ba wani soja da aka kashe a harin amma dai wasu daga cikin masu gadin wajen sun samu raunuka.

Wadanda ba sa goyon bayan gwamnatin sun ce an kashe mutane daga duka bangarorin.

Gidan talabijin na kasar Iran wato Iran Press TV ya ce an harbe daya daga cikin wakilansa dake Syrian har lahira.

Kari a kan wannan labari

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.