BBC navigation

An yankewa Marafa Hamidou hukuncin daurin shekaru 25

An sabunta: 22 ga Satumba, 2012 - An wallafa a 20:12 GMT
Paul Biya na Kamaru

An sami babban minista da laifin wawure kudade a Kamaru

An yankewa wani babban Minista a Kamaru hukuncin daurin shekaru 25 a gidan yari, bayan da aka same shi da laifin wawure dala miliyan 29 da aka ware da nufin biyan wani jirgin shugabanKasa

Kotu ta baiwa Ministan Marafa Hamidou umarni tare da wasu mutum uku, da su dawowa da gwamnatin Kasar tsabar kudi har dala miliyan 42.

A wani lokaci dai Mr Marafa Hamidou , ya taba zama daya cikin mutane masu karfin fada a ji a Kasar, kafin Shugaba Paul Biya ya sallame shi daga kan mukamin nasa a watan Disambar data gabata

Masu sukar ShugabanKasar wanda ke rike da madafun iko tun shekarar 1982, sun nuna cewa Shugaban yana amfani da batun yaki da cin hanci da rashawa, domin gujewa wadanda ka iya adawa da shi

Kari a kan wannan labari

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.