BBC navigation

Ivory Coast ta rufe iyakarta da Ghana

An sabunta: 22 ga Satumba, 2012 - An wallafa a 07:22 GMT

Shugaban Ivory Coast, Allasane Ouattara

Kasar Ivory Coast ta rufe kan iyakarta da Ghana sakamakon wasu hare-hare da aka kai a wasu wuraren bincike na soji da 'yan sandanta inda aka kashe mutane da dama.

Ministan tsaron kasar, Paul Koffo Koffi, ya ziyarci wasu wuraren da aka kai harin a ranar Juma'a, inda ya ce gwamnatinsa ta dora laifin hare-haren ne a kan wasu sojojin sa-kai da ke gudanar da harkokinsu daga kasar Ghana.

Ana zargin mutanen da ke biyayya ga tsohon shugaban Ivory Coast, Laurent Gbagbo, da kuma wasu 'yan kasar da ke gudun hijira a kasar Ghana da laifin kai wasu hare-haren a watannin da suka gabata.

Tun lokacin da aka kawar da Laurent Gbagbo daga karagar mulki, kasar ke fuskantar kalubale na tabarbarewar tsaro.

Kari a kan wannan labari

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.