BBC navigation

Ana zaman dar-dar a Damaturu da Potiskum

An sabunta: 22 ga Satumba, 2012 - An wallafa a 13:19 GMT

Wani hari da aka taba kaiwa a Damaturu.

A Najeriya yanzu haka mazauna garuruwan Damaturu da Potiskum sun shiga cikin zullumi bayan dokar hana fita na tsawon awa ashirin da hudu da gwamnatin jihar ta sanya a garuruwan biyu.

Mazauna Damaturu na bada rahotannin jin karar harbe-harbe da kuma tashin bama-bamai tun da safe, kuma jama'a sun suna cikin gidajensu.

Gwamnatin jihar Yoben dai ba ta ba hujjar kafa dokar hana fitan ba.

A baya dai jihar Yobe tayi fama da hare-hare da ake dangantawa da kungiyar nan da ake kira Boko Haram.

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.