BBC navigation

Shugabannin Sudan da Sudan ta kudu na ganawa a Habasha

An sabunta: 23 ga Satumba, 2012 - An wallafa a 16:27 GMT
Tattaunawar Sudan

Ana tattaunawa tsakanin Sudan ta Sudan ta Kudu

Shugabannin kasashen sudan da kuma sudan ta kudu na ganawa a Habasha a yau, domin kokarin warware banbance- banbancen da suka haddasa rashin jituwa tsakaninsu a farkon wannan shekarar

Wakilin BBC yace za a tattauna mahimman batutuwa da su ka hada da shata kan iyaka, da kuma rabon kudaden da ake samu daga mai, da yankin nan da ake takaddama akansa na Abiye

Sudan ta Kudu ta samu 'yancin kai daga Sudan a bara, sakamakon wata yarjejeniyar shirin samar da zaman lafiya da aka cimma, wacce ta kawo karshen yakin basasar shekara da shekaru

Majalisar dinkin duniya tayi barazanar sanyawa bangarorin biyu takunkumi idan har basu cimma wata cikakkiyar yarjejeniya ba, domin tabbatar da cewa rikicin bai sake barkewa ba

Kari a kan wannan labari

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.