BBC navigation

An tsare mata 'yan Najeriya a Saudiyya

An sabunta: 24 ga Satumba, 2012 - An wallafa a 18:14 GMT

Hukumomi a Saudi Arabia sun tsare wasu darurwan mata 'yan Najeriya da suka tafi aikin hajji, bisa zargin cewa sun tafi ba tare da muharramansu ba.

Bayanai dai na cewa matan da aka tsare sun kai dari hudu, wadanda kuma ake rade-radin cewa za a maido su gida ne.

Hukumar kula da aikin hajji ta Najeriya ta ce an samu rashin fahimta ne da hukumomin Saudiyya, amma ana kokarin warware lamarin.

Kakakin huhumar, Alhaji Uba Mana, yace jami'an hukumar na tattaunawa da hukumomin Saudiyya don kawo karshen matsalar.

Yace wasu matan sun samu damar wucewa, wasu kuma har yanzu ana can tsare dasu.

Wasu daga cikin matan da aka tsare a filin jirgi a Jeddah, Saudi Arabia, sun gayawa BBC cewa ana tsare da su ne a cikin wani daki mai sanyi.

Wata daga cikinsu tace: "A gaskiya, muna cikin ha-ula-i, an kulle mu ba-fita-ba-shiga. Ba a yi mana 'screeing' din ba; ba mu san jirgin da zamu koma da shi ba, don dai haka suke fada cewa zamu koma Najeriya. Sai mun sha yunwa tukuna a miko mana dan abinci".

Saudiyyar dai na da ka'idar cewa dole ne mace taje da muharraminta (wato mijinta, ko mahaifinta, ko dan uwa na kusa da ita sosai) kafin a ba ta iznin shiga kasar ta yi aikin hajji.

Tsarin da suke da shi da Najeriya shine jami'an kula da aikin hajjin ne suke tsaya masu a matsayin muharramansu.

Jami'an hukumar hajji a Najeriya sunce hukumomin Saudiyyar sun sanya sabbin ma'aikata ne a bana, wadanda basu san wancan tsarin ba, shi yasa aka samu matsala -- wadda su ka ce suna can suna kokarin magancewa.

Kari a kan wannan labari

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.