BBC navigation

Brahimi ya ce halin da ake ciki a Syria na kara muni

An sabunta: 24 ga Satumba, 2012 - An wallafa a 20:52 GMT
Lakhdar Brahimi

Lakhdar Brahimi

Wakilin majalisar dinkin duniya a Syria, Lakhdar Brahimi ya bayyana cewa halin da kasar Syriar ta fada ciki ba shi da kyau ko kadan, kuma lamarin na kara munana.

Ya shaida wa kwamitin sulhu na majalisar dinkin duniyar cewa ana azabtar da fursunoni, kuma jama'a na tsoron zuwa asibitocin gwamnati.

Ya kara da cewa ana fuskantar karancin abinci, tare da lalata kayan al'adun gargajiya.

Kasar Jamus, wadda ita ce ke jagorantar kwamitin, ta jaddada cewa ya kamata a samu hanyar shawo kan rikicin a siyasance, duk kuwa da cijewar al'amura a majalisar dinkin duniyar.

Sai dai mataimakin ministan harkokin wajen Syriar, Faisal Mekdad ya shaida wa BBC cewa kasarsa za ta fada wa majalisar dinkin duniya cewa kasar Turkiyya da wasu ne ke hura wutar rikicin ta hanyar tura 'yan ta'adda zuwa kasar ta Syria.

Kari a kan wannan labari

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.