BBC navigation

Obama yayi jawabi a majalisar dinkin duniya

An sabunta: 25 ga Satumba, 2012 - An wallafa a 19:13 GMT

Shugaba Obama

Shugaba Obama ya yi amfani da jawabinsa a babban taron zauran majalisar dinkin duniya wajen yin Allah wadai da tashin hanklin da ya biyo bayan wani fim din batanci ga musulunci da aka shirya a Amurka.

Obama ya kuma kara da cewa, fim din na batanci ba wai kawai ga musulunci yayi batanci ba har ma ga Amurka.

Ya kuma ce bai kamata fin din ya zama wata hujja ba ta kaiwa ofishin jakadancin Amurka a Benghazi hari ba, kuma Obama yace za'a hukunta wadanda suka kai harin.

Har ila yau shugaba Obama ya yi kiran a kawo karshen gwamnatin shugaba Bashar al-Assad Syria.

Shugaba Obama ya kuma ce, Amurka zata yi duk iya iyawarta wajen hana Iran mallakar makaman nukiliya.

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.