BBC navigation

Kananan jiragen ruwan Taiwan sun shigo huruminmu- Japan

An sabunta: 25 ga Satumba, 2012 - An wallafa a 08:06 GMT
Jiragen ruwan kasar Taiwan

Jiragen ruwan kasar Taiwan a kan teku

Kasar Japan ta ce jiragen ruwan kamun kifi daga kasar Taiwan kusan sittin ne suka shigo hurumin ruwanta dake kusa da tsibiran nan na Diaoyutai da Senkaku masu cike da takaddama dake gabashin tekun China.

Bayanai dai sun ce kananan jiragen dauke da masunta kimanin dari uku sun shigo ne domin nuna rashin amincewar su da yunkurin baya bayan nan da kasar Japan ta yi na mallakar tsibiran, wanda ya ke ci gaba da haifar da zazzafar sa-in-sa tsakanin kasashen.

Mai magana da yawun hukumar lura da gabar tekun kasar Taiwan ya ce da jijjifin safiyar Talata ne jiragen ruwan suka iso, bayan tasowarsu daga tashar jiragen ruwan dake arewacin kasar da yammacin Litinin.

Jiragen ruwa dauke da dakarun kasar Taiwan da dama ne da aka makare da makamai ke biye da kananan jiragen ruwan da ke dauke da masuntan, domin basu cikakkiyar kariya, sai dai suna da 'yar tazara kadan daga inda kasar Japan ta shata a matsayin huruminta.

Wadannan tsibirai na Senkaku da Diaoyutai masu cike da takaddama dai dukkaninsu kasashen Japan, China da Taiwan na ikirarin cewa mallakarsu ne, lamarin da ya sa dangantaka ta yi tsami tsakanin kasashen musamman na Japan da China, bayan da a makonnin baya bayan nan gwamnatin kasar ta Japan ta ce ta riga ta sayi dukkanin tsibiran a hannun wasu 'yan kasuwa.

Kawo yanzu dai babu wani fito na fito, amma kuma mai magana da yawun gwamnatin kasar Taiwan din ya ce suna da aniyar yiwa tsibiran kawanya ne, inda mai yiwuwa ne kuma za su daga tutar kasar.

Sent from my BlackBerry wireless device from MTN

Kari a kan wannan labari

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.