BBC navigation

Shugaba Mursi na Masar ya nemi a yiwa jama'ar Syria da Palasdinu adalci

An sabunta: 26 ga Satumba, 2012 - An wallafa a 20:10 GMT
Shugaba Mursi na Masar

Shugaba Mursi ya gabatar da jawabi a zauren majalisar dinkin duniya

Sabon shugaban kasar Masar, Mohammed Mursi, ya yi kira da babbar murya da a yiwa jama'ar Syria da Palasdinu adalci.

A jawabinsa na farko a zauren babban taron majalisar dinkin duniya, wanda shi ne na farko da wani zababben shugaban kasar Masar ya yi- Mr. Mursi ya ce tilas ne a tsaida zubda jinin da ake a Syria tare da shawo kan matsalar da jama'ar kasar ke ciki.

Har ila yau kuma, ya yi amfani da wani muhimmin bangare na jawabin nasa wajen tabo irin halin da Palasdinawa ke ciki shekaru aru-aru, yana mai cewa su ma ya kamata su dandana dadin 'yancin kai da girmamawa.

Ya ce batu na farko da tilasne duniya ta yi kokarin warwarewa bisa gaskiya da adalci shi ne makomar Palasdinawa.

Kari a kan wannan labari

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.