BBC navigation

Majalisar dattawan Najeriya ta nemi gwamnati ta daukaka kara kan yankin Bakassi

An sabunta: 26 ga Satumba, 2012 - An wallafa a 20:03 GMT
Shugaba Goodluck Jonathan

Ana bukatar gwamnati ta daukaka kara kan yankin Bakassi

A Najeriya, majalisar dattawan kasar ta zartar da wani kudiri da ya nemi gwamnatin Kasar ta gaggauta daukaka kara game da hukuncin da kotun kasa-kasa ta yi, wanda ya mika yankin Bakassi ga kasar Kamaru.

Majalisar ta yi zargin cewa a baya gwamnatin kasar ba ta bi ka'ida ba, kafin ta amince da mika yankin.

Majalisar dattawan dai ta zartar da wannan kudirin a daidai lokacin da shugaban Najeriyar, Dr Goodluck Jonathan ya shaida wa taron majalisar dinkin duniya cewa kasar sa za ta martaba hukuncin da kotun kasa-da-kasa ta yanke a shekera ta 2002.

'Yan majalisar dattawan Najeriyar sun bayyana cewa gwamnatin data shude ta zamanin shugaban Najeriya, Olusegun Obasanjo ta yi zumudin amincewa da hukuncin kotun duniyar, tare da mika yankin Bakassi ba tare da bin wasu ka'idoji da kundin tsarin mulkin Najeriyar ya gicciya ba.

Kari a kan wannan labari

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.