BBC navigation

Senegal na juyayin nutsewar mutane 1900

An sabunta: 26 ga Satumba, 2012 - An wallafa a 08:05 GMT
Jirgin ruwan Joola na kasar Senegal

Jirgin ruwan Joola na kasar Senegal

Al'ummar kasar Senegal dake yankin Yammacin Afirka na juyayin zagayowar shekaru goma da nutsewar jirgi ruwa, hatsarin da yasa fasinjoji kusan dubu da dari tara suka mutu.

An bayyana al'marin da cewa shi ne ya na daya daga cikin mummunan tarihi a fannin jiragen ruwa.

Jirgin ruwan mai suna Joola, na tsakanin arewaci ne da kudancin Senegal lokacin da ya nutse a tekun Atlantika.

A lokacin da jirgin ruwan na Joola ya nutse a shekarar 2002 dai, gwamnatin kasar ta danganta wannan al'amari ne da rashin kyawun yanayai, sai dai kuma sakamakon wani bincike da aka fitar bayan 'yan wasu watani, ya nuna cewar hadarin jirgin ya abku ne saboda sakaci.

Jirgin ruwan wanda ke karkashin kulawar rundunar sojojin ruwan kasar, bai cika amfani da sharuddan amfani da jiragen ruwa na kasa da kasa ba, kuma yana dauke ne da fasinjojin da suka ninka adadin wadanda ya kamata ya dauka har sau hudu.

Daga bisani dai an gabatar da batun a gaban kotu, inda aka dora alhakin abkuwar hadarin kan matukin jirgin wanda shi ma ya rasa ransa a hadarin.

Mutane 64 ne kadai suka tsira da ransu.

Kungiyar iyalan wadanda suka rasa ran su sun yi alwashin sake gabatar da batun a gaban kotu, kasancewar an sake zaben sabon shugaban kasar.

Kari a kan wannan labari

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.