BBC navigation

Majlaisar ministocin Spain na nazarin sabon tsarin tsuke bakin aljihu

An sabunta: 27 ga Satumba, 2012 - An wallafa a 16:29 GMT
Zanga zanga a Spain

Gwamnatin Spain na shirin rage kudaden da take kashewa

Majalisar ministocin kasar Spain ta kwashe awoyi da dama ta na nazarin sabon tsarin tsuke bakin aljihu, yayinda gwamnatin ke shirin bayyana shirin rage kudaden da take kashewa.

'Yan kasar ta Spain, wadanda ke fama da matsalolin tabarbarewar tattalin arziki da rashin aikin-yi, su na shirin fuskantar wasu rage kudaden da gwmantain ke kashewa, da karin albashi da kuma gyare-gyaren da zasu baiwa gwamnatin damar samun rarar dalar bilyan 50.

Amma 'yan kasar su na kokawa sosai game da wannan mataki.

Kari a kan wannan labari

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.