BBC navigation

Sudan da Sudan ta Kudu sun rattaba hannu kan wata yarjejeniya

An sabunta: 27 ga Satumba, 2012 - An wallafa a 16:07 GMT
Shugabannin Sudan da Sudan ta Kudu

An cimma wata yarjejeniya tsakanin Sudan da Sudan ta Kudu

Kasashen Sudan da Sudan ta Kudu sun rattaba hannu akan yarjejeniyar warware wasu daga cikin rikice-rikicen da su ka kai kasashen biyu wani fagen yaki a bana.

Bayan sun yi kwanaki hudu su na tattaunawa a Habasha, kasashen sun amince akan wani tsarin tattalin arziki, wanda zai bada damar fitar da mai daga Sudan ta Kudun, abi dashi ta Sudan zuwa kasashen ketare.

To amma tunda har yanzu ba a warware wasu batutuwan ba, musamman ma batun yankin Abyei, wakilin BBC a wajen taron yace yarjejeniyar bata cimma dukkanin abubuwan da ake bukata ba.

Kari a kan wannan labari

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.