BBC navigation

An kama wanda ya shirya fim din batanci ga Musulunci

An sabunta: 28 ga Satumba, 2012 - An wallafa a 07:24 GMT
Nakoula Basseley Nakoula, wanda ya yi fim din batanci ga musulunci

Nakoula Basseley Nakoula,wanda ya yi fim din batanci ga musulunci

Wata kotu a birnin Los Angeles na Amurka ta tsare mutumin da ya shirya fim din nan da yayi batanci ga addinin Islama da manzon Allah annabi Muhammad SAW, wanda ya haddasa gagarumar zanga-zanga a kasashen musulmi da dama cikin makon jiya.

An dai sanya tallar fim din ne a shafin intanet na Youtube, wanda ya harzuka musulmai a fadin duniya.

Nakoula Besseley Nakoula wanda dan asalin kasar Masar ne, kotun ta daure shi ne bayanda ta same shi da laifin keta kaidojin daurin talalar da aka yi masa kan laifin zamba a shekarar 2010.

Wani alkali ne a birnin Los Angeles ya hukunta tare da daure Nakoula Besseley Nakoula, mai kimanin shekaru 55, wanda dan asalin kasar Masar ne bayan da kotu ta same shi da aikata ba daidai ba.

Mr Nakoula ya buya ne bayan da aka zarge shi da hannu wajen hada fim din da yayi batanci da addinin musulunci mai suna ''The Innocence of Muslims'', wanda ya haifar da rudani da zanga-zanga a yankin Gabas ta Tsakiya, sai dai ya musanta cewa shi ne ya shirya tare da sanya fim din a shafin intanet na Youtube tare da amfani da suna na bogi wato '' Sam Bacile''.

A shekara ta 2010 ne aka cafke tare da tuhumarsa da karya dokar daurin talala, da suka hada da amfani da yanar gizo ba tare da neman iznin jami'i mai lura da dokar ta daurin talalar ba.

Kotun ta birnin Los Angeles dai ta haramata belin sa, inda ta umarci a ci gaba da tsare shi, don gudun kada ya samu kafar tserewa.

Gwamnatin Amurka ta gamu da kakkausar suka kan rashin daukar matakai game da fitar da bidiyon da ya haifar da zanga-zangar nuna fushi da tashe-tashen hankula a wasu kasashen musulmi.

Kari a kan wannan labari

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.