BBC navigation

Kungiyar Al Shabab ta fice daga Kismayo

An sabunta: 29 ga Satumba, 2012 - An wallafa a 17:20 GMT
Birnin Kismayo

Al Shabab tace ta fice daga Kismayo, inda suke da karfi

Wani mai magana da yawun kungiyar Al shabbab Ali Mahmoud Rage yace janyewar su daga birinin wata dabara ce kawai ta yaki.

Ya kuma yi barazanar cewar zasu sake shigowa idan har dakarun kungiyar hadin kan Afurka ta AU su ka kuskura su ka kutsa kai cikin Kismayon.

Su ma dai Sojojin Kasar Kenya na tunanin cewar watakila gadar zare suke masu.

A saboda haka har yanzu dakarun kasashen Kenyan da Somalin basu yarda sun kutsa kai cikin garin ba, amma wani mai magana da yawun rundunar tsaron Kenyan Kanal Cyrus Oguna ya fadawa BBC cewa lokaci ne kawai suke jira kafin rundunarsa wacce yanzu haka take wajen Kismayon, ta kutsa kai cikin garin.

Kafin janyewar kungiyar dai daga garin, Mataimakin Fira Ministan Kenya Musalia Mudavadi ya bayyana fafutukar da ake yi na kwato Kismayon a matsayin wani mahimmin al'amari

Magidanta a Kismayo dai yanzu haka sun tsinci kansu cikin wani birni ne da ba wanda keda iko da shi.

Akwai rahotannin kwasar ganima, bayan dan rashin kwanciyar hankalin da aka samu.

Kari a kan wannan labari

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.