BBC navigation

Kenya da Somalia na tunkarar Al_shabaab

An sabunta: 29 ga Satumba, 2012 - An wallafa a 06:56 GMT

Al shabaab

Sojojin Kasashen Kenya da Somalia na tunkarar mayakan Al Shabab masu kaifin kishin addinin islama, bayan da suka sauka gabar tekun Somalia a Kismayo- wani babban yanki dake cikin birni na karshe da 'yan tawayen suke rike da shi.

Wani mai magana da yawun gwamnatin Kenyan ya ce hadin gwiwar dakarun Kasashen biyu sun shiga bangaren arewacin birnin.

Amma mazauna yankin tsakiyar Kismayon sun gaya wa BBC cewar, har yanzu kungiyar ta Al Shabab ce ke da iko, kuma sojojin hadakar na da tazara daga wurin da ake gwabza fadan.

Wani mai magana da yawun dakarun tsaron Kenya Kanar Cyrus Oguna ya shaidawa BBC cewar korar da sojoji suka kai ta samu nasara.

Kari a kan wannan labari

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.