BBC navigation

An tsame MEK daga Kungiyoyin ta'adda

An sabunta: 29 ga Satumba, 2012 - An wallafa a 04:16 GMT

'Yan Kungiyar MEK

Ma'aikatar harkokin waje ta Amura ta bada sanarwa a Washington cewa Kasar Amurka ta tsame 'yan adawa na Kungiyar MEK a Iran daga jerin 'yan ta'adda.

Ma'aikatar ta ce Sakatariyar harkokin wajen Amurka Hillary Clinton ta yi la'akari ne da janyewar duk wani tashin hankali da Kungiyar ta MEK ta futo karara tayi.

Ma'aikatar harkokin wajen ta Amurka ta ce ba ta dauke kai daga aiyukan ta'addanci da Kungiyar ta MEK tayi a baya ba, haka kuma ana nan ana ci gaba da sa ido a kan su sosai.

Amma Kungiyar ta MEK yanzu ba ta cikin jerin Kungiyoyin 'yan tadda a Ma'aikatar, wannan na nufin ke nan za'a sakar musu da kadarorin su kuma Amurka zata iya haduwa da su tayi kasuwanci da su.

Kungiyar MEK dai ta yi yakin sunkuru da gwamnatin Shah ta Iran a shekara ta alif dari tara da sabain, ta kuma soki shugabanci na malamai a kasar ta Iran daga tushen ta da yake a kasar Iraqi.

Ta jima tana samun tallafi daga majalisar dokokin Amurka kuma an sha rawaitowa cewa Kungiyar ta MEK tana bada bayanan sirri ga Amurka kan shirin Iran na Nukilya.

Kari a kan wannan labari

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.