BBC navigation

Gobara ta tashi sakamakon gumurzu a Aleppo

An sabunta: 30 ga Satumba, 2012 - An wallafa a 05:29 GMT

Gobara a Aleppo

Wata gobara da ta tashi sakamakon gumurzun da ake yi tsakanin 'yan tawaye da sojojin gwamnatin Syria a birnin Aleppo ta lalata mafi rinjayen tsohuwar kasuwar garin.

Tsohon birnin na Aleppo yana daya daga cikin wuraren tarihi dake karkashin kulawar hukumar kula da ilimi, kimiyya da al'adu ta Majalisar Dinkin Duniya UNESCO.

Wurin da gobarar ta tashi ya kunshi wasu kananan hanyoyin cikin duwatsu da 'yan shaguna da aka yi da katakai.

Wani hoton video da aka saka a hanyar sadarwa ta internet ya nuna gobarar tana kurmushe daya daga cikin kasuwanni masu dimbin tarihi da suka rage a yankin gabas ta tsakiya.

A ranar alhamis, 'yan tawayen suka kaddamar da abinda suka bayyana cewar fada ne na a yi ta ta kare.

Kari a kan wannan labari

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.