BBC navigation

Shugaban Burma ya dauki Suu kyi a matsayin abokiyar aiki

An sabunta: 30 ga Satumba, 2012 - An wallafa a 04:13 GMT

Aung San Suu Kyi

Shugaban kasar Burma Thein Sein ya shaidawa BBC cewa yanzu ya dauki jagorar adawar sa Aug Sang Suu kyi a matsayin abokiyar aikin sa.

Shugaban ya ce idan mutanen Burma suka ce suna so ta zama shugabar kasar Burma a zabe mai zuwa zai amince da hakan.

Shugaba Thein Sein babban mamba ne na gwamnatin soji mai danniya na kusan tsawon shekaru ashirin a kasar ta Burma.

Yanzu Shugaban ya zama mai ra'ayin kawo sauyi a tsarin siyasar kasar.

Shugaba Thein ya shaidawa BBC cewa sauyi daga mulkin danniya zuwa na Dimokradiyya aiki ne da son alumma.

Sakon sauye-sauye na shugaba Thein Sein ya karawa gwamnatin shugaba Obama kwarin gwiwa da ya sa Amurka ta sassautawa Kasar Burma takunkumin kasuwanci.

Abin tambayo a nan shi ne shin ko wannan sauye-sauyen zai sa daga karshe Aung Sang Suu Kyi ta zama shugabar kasa?

Farkon lamarin na nuna alamun hakan sosai.

Kari a kan wannan labari

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.